Kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwa a jiya Talata, inda ya yi Allah wadai da babbar murya game da hare haren da aka kai wa ofisoshin jakadancin kasashen Koriya ta kudu da Morocco dake kasar Libiya, tare da nanata cewa, dole ne a gurfanar da wadanda ke da hannu cikin hare haren a gaban kotu.
Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu na MDD na Allah wadai da duk wani nau'in farmaki kan ofisoshin jakadanci, kana dole ne a kawar da kalubalen da laifuffukan ta'addanci suke kawo wa zaman lafiya da tsaron kasashen duniya.
Ban da haka kuma, sanarwar ta ce, kwamitin sulhu na MDD ya nanata bukatar bin ka'idar " magance kai farmaki ga ofisoshin jakadanci" da kuma nauyin kare su dake bisa wuyan gwamnatocin kasashen da ofisoshin suke kasancewa.
A Lahadi 12 ga wata, wasu mahara sun harbe masu gadi biyu a gaban kofar ofishin jakadancin Koriya ta kudu dake kasar Libiya. Sannan kuma a ranar Litinin, an kai harin boma-bomai kan ginin ofishin jakadancin kasar Morocco dake wannan kasa ba tare da raunatar wani ba. (Lami)