A jiya Lahadi, ana ci gaba da musayar wuta a tsakanin dakarun kungiyar Fajr Libya na kasar Libiya da 'yan kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi a birnin Sirte dake arewacin kasar Libiya, inda aka samu mutuwar mutane a kalla 20.
Wani 'dan kungiyar Fajr Libya ya gaya wa manema labaru cewa, domin taimakawa sojojin kasa na kungiyar, jiragen saman soja na kungiyar sun kai farmaki ga wani sansanin kungiyar IS. Ya zuwa yanzu, bangarorin biyu na musayar wuta mai tsanani a wurare da dama na birnin Sirte.
Wannan mutum ya kara da cewa, tun daga ranar 14 ga wata da aka fara yakin, an kashe 'yan kungiyar IS 18, yayin da wasu 15 suka ba da kai. A bangare na daban, 'yan kungiyar Fajr Libya 2 sun mutu.(Lami)