A daren jiya Litinin, kwamitin sulhu na MDD ya kalubalanci bangarori daban daban na kasar Libiya da su cimma matsaya daya kan aikin kafa wata hadaddiyar gwamnatin kasar a lokacin taron musayar ra'ayi nasu a karo mai zuwa, domin kawo karshen rikicin kasar.
A cikin sanarwar da ta fitar ma manema labaru, ta ce, kwamitin sulhun ya lura da ganawar da shugabannin bangarori daban daban na kasar suka yi a ranar Litinin a kasar Algeria, ban da haka kuma ana sa ran ganin gudanar taron musayar ra'ayi kan batun Libiya karo mai zuwa, wanda manzon musamman na babban sakataren MDD Bernandino Leon ya sa kaimi ga gudanar da shi a Laraba 15 ga wata a kasar Morocco.
Ban da haka kuma, kwamitin sulhu na MDD ya dora muhimmanci sosai kan tarzomar dake faruwa a kasar Libiya, ya kuma jaddada cewa, ba za a kawo karshen rikici ba ta hanyar daukar matakan soja. Ya yi kira ga bangarori daban daban da su daina nuna adawa da juna domin kafa kyakkyawan muhallin yin shawarwari cikin lumana.
Kana kwamitin sulhun ya nuna cewa, bisa kudurin da aka zartas, kwamitin a shirye yake wajen sanya takunkumi ga wadanda suka tada rikici da kawo barazana ga yunkurin shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Libiya.(Lami)