Shiga cikin tsarin manyan kudade na hada hada na DTS ya kasance wani muhimmin mataki domin ganin kudin Renminbi ya zama wani kudin ajiya na duniya.
A lokacin bazara, IMF za ta sake duba ma'aunin kudin da suka kunshi tsarin DTS, wanda yake kunshe a halin yanzu da dalar Amurka, Yen kudin Japan, Fan kudin Burtaniya da Euro kudin tarayyar Turai.
Haka ma a wannan wata, IMF ya sanar da cewa Renminbi ba ya cikin kudin din ba'a karya darajarsu ba, kuma kungiyar na maraba da raba da mukasudin kasar Sin dake da manufar shigar da Renminbi cikin tsarin DTS haka kuma tana son yin aiki a wannan hali tare da hukumomin kasar Sin. (Maman Ada)