in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karancin man fetur ya haifar da manyan matsaloli a Nijeriya
2015-05-27 16:22:44 cri

Najeriya kasa ce da ke kan gaba a daukacin nahiyar Afirka a fannin samar da albarkatun man fetur, amma duk da haka a baya-bayan nan ta sha fama da matsalar karancin man fetur, lamarin da ya haifar da babbar illa ga tattalin arzikin kasar, tare da gurgunta sauran al'amura na yau da kullum.

Najeriya ta fuskanci matsalar karancin man fetur har tsawon wata guda ko fiye. 'Yan kwanaki kadan da kammala zaben shugaban kasar a watan Afrilun da ya shude, babban birnin kasar Abuja, da babbar cibiyar tattalin arzikin kasar dake Lagas, da ma sauran biranen kasar sun fada cikin wannan matsala. Ya zuwa karshen makon jiya, tasirin da hakan ya haifar ya yi matukar kazanta.

Da farko, matsalar ta kawo babbar illa ga sha'anin sufuri, inda da dama daga gidajen mai dake babban birnin kasar suka rurrufe, kana sufurin manyan motocin fasinja ya tsaya tsak. Kaza lika wannan matsala ta haddasa dakatar da zirga-zirgar wasu daga jiragen sama a kasar. An ce, an dakatar da zirga-zirgar da ta kai kashi 80 cikin dari na jiragen saman dake zirga-zirga a cikin kasar, yayin da kuma jiragen sama na kasashen waje suka rika canja hanyar su zuwa kasashen Senegal, da Ghana, da Benin dake makwabtaka da Najeriyar domin ci gaba da hada-hadar su.

Haka zalika kuma, matsalar karancin man fetur ta tsananta halin da ake ciki na karancin wutar lantarki a kasar. Ta yadda tasoshin samar da wutar lantarkin kasar suka koma samar da wutar da bata wuce kashi daya cikin hudu ba. Wannan mataki dai ya sa sassan kasar da dama fadawa matsalar rashin wutar lantarki.

Hakan ne kuma ya sanya kamfanin sadarwa na MTN dake hada-hada a kasar bayyana rage lokacin bada hidimar sa ga 'yan kasar a kowace rana. Kana wasu gidajen rediyo dake kasar sun dakatar da gabatar da shirye-shirye, baya ga bankuna, da kamfanoni, da hukumomin gwamnatin kasar da suma suka rage lokacin gudanar da aikinsu a sakamakon wannan matsala.

Ana dai iya cewa, wannan matsala ta rashin isasshen man fetur, ta jefa tattalin arzikin Nijeriyar cikin wani mawuyacin hali.

Rahotanni dai sun nuna cewa wannan matsala na da alaka da yajin aiki da ma'aikatan kungiyar masu dakon man fetur suka shiga tun daga karshen makon jiya, kafin daga basani a fara babban yajin aikin da ya game dukkanin sassan ma'aikatan man fetur dake kasar. Hakika dai, akwai alamar samun wannan matsala tun daga ranar 28 ga watan Maris da ya gabata.

Baya ga wannan matsala ta karancin man fetur da ta tsananta, ta kuma haifar da babbar illa ga tattalin arzikin kasar ta Nijeriya, a hannu guda hakan ya kara haifar da wasu matsalolin na daban a kasar. Ga misali masanan tattalin arzikin kasar sun yi kashedin cewa, mai yiwuwa ne wannan matsala ta rage imanin da masu zuba jari na kasashen wajen ke da shi a kan Najeriyar, wanda hakan ka iya yin mummunan tasiri ga farfadowar tattalin arzikin kasar.

Ban da kalubalen da kasar ta fuskanta a fannin tattalin arziki, matsalar karancin man fetur ita ma ta kawo illa ga siyasar kasar. Inda shugaban kasar na yanzu wanda kuma ke daf da sauka daga karagar mulki a ranar Juma'a wato Goodluck Jonathan, ke shan suka daga sassan masu ruwa da tsaki. Wasu ma na zargin cewa gwamnatin Jonathan ta tsara wannan matsala ne ta rashin man fetur da gangan. Yanzu ke nan , sabon shugaban kasar mai jiran gado wato Muhammadu Buhari, da gwamnatin sa su na fuskanci fuskantar kalubale a fannin tattara kudaden shiga don warware matsalolin dake addabar kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China