in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai sauran rina a kaba wajen komar da 'yan gudun hijiran Nijeriya gidajensu
2015-04-15 16:50:21 cri

Har kullum fararen hula ne ke dandana kudar matsalolin dake nasaba da ta'addanci, a kasar Nijeriya dake yammacin Afrika, kungiyar Boko Haram na ci gaba da addabar kasar, ya zuwa yanzu, harin ta'addanci da aka kai a kasar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 10, kana mutane kimanin dubu 100 suka bar gidajensu.

Jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin kasar Nijeriya, na daya daga cikin jihohin da hare-haren ta'addanci suka fi kamari a wurin. Tun daga shekarar 2014, bayan da yanayin tsaro dake wurin ya ci gaba da tsananta, kungiyar Boko-Haram ta mamaye akasarin wuraren dake yankin arewacin jihar, wanda ya sa 'yan gudun hijira da dama suka bar gidajensu, suka gudu zuwa yankin kudancin kasar. Bisa kokarin tsugunar da wadannan 'yan gudun hijira, tun daga watan Nuwamba na bara, gwamnatin Nijeriya ta fara kafa sansanonin 'yan gudun hijira a birnin Yola hedkwatar jihar Adamawa, yayin da wakilinmu ke shiga sansanin Mayolkoh da ke wurin, wata jami'ar dake kula da sansanin, Rowna ta gaya mana cewa,"'yan gudun hijira da dama da suka fito daga yankin arewacin jihar suna zama a nan, inda ake iya tabbatar da tsaronsu, da kuma samar musu abinci da ruwan shan na kyauta. Kana akasarinsu mata da yara ne, zaman rayuwarsu a nan yana da kyau."

Ban da abinci ma, kome na gudana yadda ya kamata a wannan sansani, wani ma'aikacin hukumar ko-ta-kwana ta Nijeriya Zakari ya gaya wa wakilinmu cewa,"Duba, akwai abinci, sukari, da mai a wurin. Ga can kuma, akwai gidaje, kuma akwai wurin adanan kayayyaki. Ban da wannan, akwai wani injin samar da wutar lantarki, da wani karamin asibiti, har ma da wata makaranta."

Ban da sansanin Mayolkohi, ana iya samun sauran sansanoni uku da ke kusa da wurin, wadanda suka taba tsugunar da mutane sama da 2000. Sakamakon tsanantar halin da ke ciki a yankin arewa maso gabashin kasar, kungiyar Boko Haram ta mamaye manyan wurare, hakan ya sa 'yan gudun hijira suka yi ta kwarara zuwa sansanonin wurin. Mohammed Ali da ya fito daga yankin arewacin jihar Adamawa ya kasance daya daga cikinsu, ya ce,"An yanke ma goggota wuya, diyata ma aka harbe ta da bindiga. Don haka mun gudu daga garinmu, amma akwai wasu tsoffin da ba su iyar fitowa ba, sun tsaya cikin garin. Ya zuwa yanzu dai watanni takwas sun wuce, ba mu da duriyarsu. Da farkon zuwanmu a nan, yaranmu su kan je bara, akwai mutane masu kirki da dama da suka ba su kudi. Bayan da muka samu kudin, sai muka je mu sayo ruwa domin mu bai wa yara su sayar da su a kan titi."

Mohammed Abdullahi, malami ne na wata makarantar firamare, dake zaune a yankin karkarar Yola, wanda ya karbi 'yan gudun hijira 22 don su zauna a gidansa, yanzu, suna zaman kashe-wando. Ya ce,"'Yan gudun hijira da suka yi zama a gidana, na ba su abinci da wurin kwana. Sabo da ina dogoro kawai da albashina, don haka, ban iya ba su babban taimako ba sai dai bisa gwargwadon karfina. Yanzu, wata babbar matsala gare ni ita ce, an ba da kudin agajin kasashen duniya ga sansanonin da gwamnatin ta kafa kawai, ba a ba mu ko sisi ba."

Duk da mawuyacin hali da suke ciki, duk 'yan gudun hijira suna da buri guda, wato komawa gidajensu tun da wuri. Tun daga watan Maris na bana, sojojin hadaka dake kunshe da sojojin gwamnatin Nijeriya da na kasashen Chad, Nijer, da Cameroon suka fara kai farmaki kan kungiyar Boko Haram. Kuma a makwanni biyu da suka gabata, sojojin sun sanar da karbe duk jihar Adamawa, amma har yanzu, akwai rashin tabbas game da yanayin tsaron na wurin. Bugu da kari, sakamakon yin gudun hijira cikin dogon lokaci, wadannan 'yan gudun hijira ba su da ko kwabo, har ma ba su san me za su yi don ci gaba da zaman rayuwarsu bayan da suka koma garuruwansu. Ali ya ce, "Ina so in koma, yau ma an kira mu, amma ba mu da kudin komawa, sai dai gwamnati ta tura wata mota don kwashe mu, ina rokon Allah ya saukin wannan matsala. Allah ya sa mu koma gida, samu walwala, kamar a lokacin da."

Yayin da wakilimu ya bar wurin, yaran da ke sansanin 'yan gudun hijira sun fara rera wakoki. Ga wadannan yara, ba su san laifin ta'addanci ko yake-yake ma, kuma ba su fahimci ma'anar 'yan gudun hijira ba, watakila wannan dalili ne da ya sa suka iya jin dadin zamansu na yanzu kamar haka. Cikin sahihanci ne muna fatan nan ba da dadewa ba, za su iya komawa gidajensu, don ci gaba da jin dadin zaman rayuwa cikin walwala da fara'a.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China