in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shekara daya da sace 'yan matan Chibok a jihar Borno
2015-04-15 17:23:35 cri


Ranar 14 ga wata, rana ce ta cika shekara daya cif da sace 'yan matan Chibok fiye da dari biyu da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram suka yi. A wannan rana, wasu matasa da iyayen 'yan matan sun gudanar da taron gangami da zanga-zangar cikin lumana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Wakilinmu Murtala dauke da karin bayani.

An fara zanga-zangar lumana ne tun daga safiyar ranar Talata, inda wasu matasa da mambobin kungiyar Bring Back Our Girls da kuma iyayen 'yan matan Chibok da aka sace suka nufi ma'aikatar ilimi ta tarayya, domin bayyana bukatunsu ga hukumomin kasar.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar nan mai suna Bring Back Our Girls Hajiya Hadiza Ibrahim ta bayyana cewa:

Shi kuma a nasa bangaren, daya daga cikin masu zanga-zanga, kana mahaifin wata yarinyar da aka sace daga garin Chibok na jihar Borno, malam Abana Mutha ya bayyana ra'ayinsa kamar haka:

Ko da yake gwamnatin Goodluck Jonathan mai barin-gado ta ce tana iyakacin kokarinta wajen kubutar da wadannan 'yan mata, amma har yanzu ba'a da duriyarsu. Sai dai akwai wasu jita-jitar dake nuna cewa, an riga an hallaka su, wasu kuma sun ce suna raye, wasun ma sun ce 'yan matan suna Gwoza da kuma dajin Sambisa dake kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Game da haka, Dokta Bawa Abdullahi Wase, wani masanin harkar tsaro a Najeriya cewa yayi:

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China