in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Chadi sun kashe mayakan Boko Haram 207
2015-02-25 14:21:31 cri

Bisa kiyasin karshe na baya bayan nan, mayakan kungiyar Boko Haram ta Najeriya 207 aka kashe a ranar Talata, a yayin wani gumurzu tare da sojojin kasar Chadi dake fafatawa a doron kasar Najeriya, in ji hedkwatar sojojin kasar Chadi a gidan talabijin din kasar a ranar Talata.

Mun karbi kayayyakin yaki masu tarin yawa, da suka hada da wani tankin yaki mai dauke da na'urar karbar bayanai, rokoki biyu, motoci kirar Pick-up biyu, kananan makamai da miliyoyin harsasai da sauransu, in ji wannan sanarwa tare da kara cewa, an lalata wasu karin motoci kirar Pick-up da babura da dama.

Sai dai sojojin Chadi sun samu asarar mutuwar soja guda, sojoji uku da harsashi ya raunana da kuma wasu shida da suka jikkata sakamakon wani hadari.

Bayan musanyar wuta mai tsanani a tsawon sa'o'i da dama, sojojinmu sun murkushe abokin gaba kwata-kwata, in ji wannan sanarwar hedkwatar sojojin kasar Chadi.

Tun shiga yaki da kungiyar Boko Haram a tsakiyar watan Janairun shekarar 2015, sojojin Chadi sun samu nasarar kwato garuruwan Gambaru da Dikwa daga hannun kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China