Ministan sadarwa na kasar Chadi Hassan Bakari Sylla ya bullo da dabarar sadarwa ta yaki da kungiyar Boko Haram a ranar Litinin a makarantar aikin jarida ta IFTIC da ke birnin Niamey a yayin ziyarar aikinsa a kasar Nijar. Ministan ya samu tattaunawa tare da kungiyar daliban kasar Chadi dake IFTIC, wanda kuma ta mika bukatun daliban ga minista Bakari Sylla.
Ban zo nan ba domin ganawa kawai da daliban Chadi, amma na zo domin ganawa da dukkan matasan Afrika domin su ba mu taimako wajen yaki da Boko Haram ta hanyar sadarwa, musammun ma ta hanyar shafukan sada zumanta, in ji mista Bakari Sylla yayin da yake ba da amsa kan sakon da daliban Chadi dake IFTIC suka gabatar masa.
Mu yi amfani da dukkan hanyoyin da muke da su kamar shafukan sada zumanta, in ji ministan Chadi, domin nunawa Aboubacar Shekau da mayakansa cewa, abubuwan da suke aikatawa ba musulunci ba ne.
Don haka, hada karfi da karfe domin gudanar da ayyuka, na bukatar hadin gwiwa tsakanin masu aikin sadarwa na kasashen da suka shiga yaki da Boko Haram. Daga bisani kuma, minista Bakari Sylla ya jinjinawa darekta janar na IFTIC, Khamed Abdoulaye, a matsayin wani babban mai fada a ji da ya daga tutar wannan makaranta, da ta kasance wata makarantar ba da misali. (Maman Ada)