in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nijar da Chadi sun kwato Damasak da Malafatori daga hannun Boko Haram
2015-03-10 10:46:02 cri

Sojojin Nijar da na Chadi sun kwato yankunan Damasak da Malafatori na Najeriya dake kusa da iyaka da kasar Nijar, da suka jima a karkashin kungiyar Boko Haram yau da kusan watanni da dama, a ranar Lahadi bayan wani babban samamen taron dangi da suka kai kan kungiyar Boko Haram, in ji wata majiya mai tushe a ranar Litinin a Niamey.

A cewar gidan rediyon Amfani, wata kafa zaman kanta, da ta ba da wannan labari a ranar Litinin, ta ce, karbe wadannan yankuna daga hannun Boko Haram, ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan kungiyar da dama a yayin da wasunsu suka tsere a gaban luguden wutar sojojin Nijar da na Chadi.

A wannan gumurzu na rana ta farko da Boko Haram, sojoji 29 ne suka ji rauni, daga cikinsu akwai sojojin Nijar 6 da na Chadi 23, kuma dukkan na samun jinya a asibitin jihar Diffa.

Haka kuma an cakfe mutane da dama dake da alaka da kungiyar Boko Haram a yankunan Nijar da suka hada da Nguigmi da Bosso dake iyaka da Najeriya.

Sojojin Nijar da Chadi sun kaddamar tun a safiyar Lahadi da wannan babban samame ta sama da ta kasa kan kungiyar Boko Haram a Najeriya, tun daga bakin Diffa da Bosso dake kudu maso yammacin Nijar, dake iyaka da Najeriya.

Majiyoyin tsaro sun ce, dubun dubatar sojoji ne aka tura, da daruruwan makaman yaki da kuma tankokin yaki wajen kai wannan samame kan kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China