Yawan kwal da aka yi amfani a cikin tsarin kashe makamashi a birnin Beijing ya ragu zuwa kashi 20 cikin dari
Gaggauta rage yawan kwal da aka yi amfani da bunkasa makamashi mai tsabta su ne ayyuka masu muhimmanci na birnin Beijing don kyautata tsarin makamashi da ingancin yanayi. A bana, za a kayyade yin amfani da kwal a birnin Bejing zuwa ton miliyan 15. Ya zuwa karshen shekarar 2014, yawan kwal da aka yi amfani a cikin tsarin rage makamashi a birnin Beijing ya ragu zuwa kashi 20 cikin dari, yawan makamashi mai tsabta da aka yi amfani da su ya kai kimanin kashi 80 cikin dari.
Mataimakin shugaban sashen raya makamashi na kwamitin raya birnin Beijing da yin kwaskwarima Wang Yuming ya bayyana a gun taron kwamitin kiyaye muhalli na birnin a yau Litinin cewa, ya zuwa karshen shekarar 2014, yawan makamashin da za a iya sake yin amfani da su a cikin tsarin makamashi na birnin Beijing ya kai kashi 5.5 cikin dari, yawan wutar lantarki da aka samar ta hanyar hasken rana ya kai kimanin kilowatt dubu 200, kuma farin wurin da aka yi amfani da makamashin zafin kasa ya zarce muraba'in mita miliyan 46. (Zainab)