Ministan ma'aikatar kudin kasar Ghana Seth Terkper, ya yi hasashen farfadowar tattakin arzikin kasarsa nan da wani dan lokaci. Mr. Terkper ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin wani taron masana da kwararru a fannin tattalin arziki da ya gudana a birnin Accra.
A cewarsa, tattalin arzikin Ghana ya samu bunkasa zuwa matsayi na koli da kaso 15 bisa dari a shekarar 2011, kafin ya yi mummunar faduwa zuwa kaso 4.4 a bara. Sai dai duk da halin da ake ciki a yanzu haka, ministan ya ce, ana sa ran dagawar mizaninsa da kaso 8 cikin dari, sama da hasashen da aka yi a baya.
Sai da fa Mr. Terkper ya ce, dole a dauki wasu muhimman matakai, idan har ana da son cimma wannan buri, ciki hadda ririta kudade, da kare tattalin arzikin kasar daga almundahana. (Saminu)