Sakamakon cunkoson da ake fuskanta a filin saukar jiragen sama na Tribhuvan dake birnin Katamandu, ba a iya jigilar tantunan ta jiragen sama kai tsaye daga Sin zuwa Nepal ba. Wannan ya sa aka shafe kwanaki 14 wajen yin jigilar tantunan ta manyan motoci tare da jiragen sama.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, adadin tantunan da kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin za ta bayar ya kai 1600, wadanda za a rarraba su ga kungiyar addinin Buddha ta kasar Nepal da wasu hukumomin da abin ya shafa tare da wuraren tsugunar da jama'a dake tsakiyar birnin Katmandu. Hakazalika kuma, za a kai wasu tantunan zuwa wasu kauyukan dake nesa da birnin don taimakawa mazauna kauyukan.
Tun ranar 25 ga watan Afrilu wato lokacin da girgizar kasa mai karfin maki 8.1 bisa ma'aunin Richter ta abkawa kasar Nepal zuwa yanzu, rukunin sojojin sama na kasar Sin ya shafe kwanaki 19 yana yin jigilar kayayyakin bukatar gaggawa ga wadanda wannan bala'i ya shafa, wannan aiki ne mafi girma da kuma wuya a tarihi da sojojin saman kasar Sin suka gudanar wajen yin jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje don bada taimako. (Zainab)




