in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harkokin cinikayyar Sin za su inganta a zango na biyu na wannan shekara
2015-05-10 15:58:32 cri
Ma'aikatar cinikayyar kasar Sin, ta yi hasashen bunkasar harkokin cinikayya cikin watanni 4 na biyu na wannan shekarar da muke ciki, bayan koma bayan da aka samu a farkon shekarar.

A cewar kakakin ma'aikatar Sun Jiwen, hada-hadar fitar da kayayyaki ta ci gaba da samun tagomashi, yayin da kuma ta shigo da kayayyaki cikin kasar ta ja baya.

Bisa alkaluman kididdiga, daukacin hada-hadar cinikayyar waje ta ragu da kaso 7.6 a farkon shekarar ta bana. Cikin wannan adadi hada-hadar fitar da kaya ta daga da kaso 1.6 bisa dari, yayain da kuma ta shigo da kayayyaki ta yi kasa da kaso 17.3 bisa dari. Hakan a cewar Mr. Sun tasiri ne na faduwar darajar manyan kadarori kamar danyen-mai, da karafa, da roba da dai sauran su.

Bisa wannan alkaluma, kididdiga ta nuna cewa kamfanonin kasar ta Sin sun samu rarar kudade da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 63.4., baya ga raguwar kudaden gudanarwa, da kuma daidaita matsayin takara da kamfanonin suka samu.

A cewar kakakin na ma'aikatar cinikayya, hukumomin kasar Sin za su ci gaba da daukar matakan daidaita al'amura a fannin tattalin arziki da cinikayya, domin sauya halin koma baya da ake fuskanta a yanzu haka. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China