in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zama kasa ta farko wajen yawan yin rajistar tambarin cinikayya a duniya a shekaru 12 da suka gabata a jere
2014-09-02 14:15:37 cri
Kasar Sin ta zama kasa ta farko wajen yawan yin rajistar tambarin cinikayya a duniya a shekaru 12 da suka gabata a jere. Shugaban hukumar kula da harkokin ciniki da kasuwanni ta kasar Sin Zhang Mao ya bayyana a ranar 1 ga wata cewa, ya zuwa karshen watan Yuni na bana, yawan tambarin cinikayya da kasar Sin ta roka ya kai miliyan 14 da dubu 257.

Zhang Mao ya bayyana hakan ne yayin bikin murnar cika shekaru 20 da kafa kungiyar tambarin cinikayya ta kasar Sin kana dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin tambarin cinikayya na kasar Sin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta kafa dokokin da suka shafi tambarin cinikayya da suka dace da halin musamman na kasar da ma ka'idojin kasa da kasa, kuma kasar ta Sin tana daya daga cikin kasashe masu karfin tabbatar da ikon mallakar tambarin cinikayya a fadin duniya.

Hakazalika, Zhang Mao ya yi nuni da cewa, idan aka kwatanta Sin da sauran kasashe masu karfin arzikin masana'antu na duniya, akwai gibi sosai a tsakaninsu da kasar Sin a fannin karfin takarar tambarin cinikayya, don haka akwai bukatar kara sa lura kan muhimmancin bunkasuwar tambarin cinikayya a kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China