in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An wallafa wani bayanin da shugaban kasar Sin ya rubuta a wata kafar watsa labaru ta kasar Rasha
2015-05-07 15:32:53 cri

An wallafa wani bayani mai taken "tunawa da tarihi da kafa makoma" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta a Jaridar nan ta kasar Rasha wato "Russian Gazeta", gabanin ziyararsa a kasar don halartar bikin tunawa da ranar cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kiyaye kasar Rasha.

Bayanin na nuna cewa, yakin da masu ra'ayin Fascist da masu ra'ayin nuna karfin soja suka tada ya kawo babbar illa ga kasashen Sin da Rasha da sauran kasashen Asiya da Turai da ma sauran yankunan duniya da kuma jama'arsu. Bisa hadin kan jama'ar kasashen Sin da Rasha da kuma sauran kasashe fiye da 50, a karshe sun cimma nasarar yaki da masu hare-hare, gami da shimfida zaman lafiya a duniya.

Bayanin ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, an fi samun kyakkyawan sharadi wajen kiyaye zaman lafiya da tabbatar da bunkasuwa, don haka, ya kamata a kara kokari wajen kafa sabuwar huldar kasa da kasa don moriyar juna. Haka zakila, kamata ya yi kasashe daban daban su hada muradunsu da na sauran kasashe tare bisa ka'idar cimma nasara tare, da zama tsintsiya madaurinki daya, a kokarin tinkarar batutuwan da suka shafi sauyin yanayi da tsaron makamashi da albarkatu da tsaron internet da kuma karuwar yawan bala'u masu tsanani, ta yadda za a iya kiyaye duniya da bil Adam ke zama a ciki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China