Hadin-gwiwar Sin da Najeriya ta fuskar cinikayya na bunkasa cikin sauri
|
A ranar Alhamis 29 ga wata ne, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani dangane da hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin tattalin arziki da cinikayya, inda aka bayyana dalla dalla game da ci gaban dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Afirka tun daga shekara ta 2010. Game da wannan batu, wakilinmu Murtala ya ziyarci ma'aikatar masana'antu, cinikayya da zuba jari ta Najeriya dake birnin Abuja, inda ya samu damar hira da malam Bawa Lere Lawal, wani babban jami'in dake kula da sashin cinikayya, don jin ta bakinsa game da bunkasar huldar cinikayya tsakanin Sin da Najeriya a wadannan shekaru. Ga cikakken rahoton da ya hada mana.