in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusoshin gwamnatocin kasashe daban daban da wakilan manyan kamfanoni na kasa da kasa sun nuna kyakkyawan fatansu game da shiga babban shirin "ziri daya da hanya daya"
2015-04-20 16:10:23 cri

Jami'an diplomasiyya na kasashe daban daban da ke kasar Sin, da kuma wakilan manyan kamfanonin kasa da kasa da yawansu ya zarce 300 sun taru a nan Beijing a 'yan kwanakin nan, domin sauraron bayanin da kwararru suka gabatar kan babban shirin "zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21" wato "ziri daya da hanya daya" a takaice, inda suka bayyana kyakkyawan fatansu na inganta hadin gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin don cimma nasara tare.

A kwanakin baya ne sashen yin cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya shirya wani taron musamman kan babban shirin "zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21" wato "ziri daya da hanya daya", inda wani jami'in sashen kula da ayyukan raya yammacin kasar Sin na kwamitin raya kasa da kwaskwarima na kasar Ou Xiaoli, da kuma babban sakataren kwamitin ilimi na kasar Sin Zhang Yansheng, suka yi wa jami'an diplomasiyya su 198 daga kasashe 130 da ke nan kasar Sin, da kuma wakilai 137 na manyan kamfanonin kasa da kasa 109 bayani game da wannan babban shirin.

Yayin da yake amsa tambayar da wakilin kamfanin Mitsubishi na kasar Japan ya yi, Zhang Yansheng ya ce, manyan kamfanonin kasa da kasa ciki har da kamfanonin kasar Japan, za su samu damar cin moriya daga shirin "ziri daya da hanya daya" ta hanyar hadin gwiwa tare da gwamnatin kasar Sin, da kuma kamfanonin kasar, baya ga inganta kwarewarsu a fannin samun ci gaba a kasuwannin kasar Sin. Yana mai cewa,

"kamfanonin kasar Japan sun dauki jagoranci wajen raya ayyukansu a ketare. Tun daga shekaru 80 na karnin da ya gabata, kudin Japan ya fara shiga cikin kasuwannin kasa da kasa, kana kamfanonin kasar Japan suka fara zuba jari a ketare, duk wadannan sun zama abin koyi ga kasar Sin. Yanzu muna nazari kan hanyoyin da kamfanonin Japan suka bi, da kuma fasahohin da suka samu a fannin hadin gwiwa tare da yankuna daban daban. Don haka, ana iya ganin cewa, ba kawai kasashen da ke kan hanyar siliki ne za su samu damar bunkasuwa ba, a'a, shirin 'ziri daya da hanya daya' zai samar da damar iri daya ga kamfanonin Japan, da na Amurak da Turai.

Bugu da kari, shugaban wani kamfanin kasar Amurka da ke cikin kamfanoni mafiya nagarta 500 na duniya, ya taba yi mana tambaya cewa, yaushe ne Sinawa za su mai da kamfaninmu a matsayin na kasar Sin? A hakika, za a mai da wadannan kamfanoni a matsayin wani muhimmin kashi na wannan babban shiri."

Bisa labarin da wakilinmu ya samu, an ce, manyan kamfanonin kasa da kasa masu halartar taron sun nuna kyakkyawan fata ga sa hannu a cikin shirin "ziri daya da hanya daya". Babbar manaja mai kula da harkokin yin cudanya da gwamanati, da aikin samun dauwamammen ci gaba ta reshen kamfanin samar da kayayyakin lantarki na Schneider dake nan kasar Sin, Madam Pei Jinlin ta furta cewa,

"Mun halarci wannan taro cike muke da fatan kyautatuwa, ban da sauraron bayani kan manufofin da shirin ya shafa, muna son sanin yadda gwamnatin kasar Sin za ta baiwa kamfanonin kasashen waje da ke kasar Sin jagoranci, wajen sa hannu a cikin shirin 'ziri daya da hanya daya', a kokarin sa kaimi ga ci gabanmu."

Li Cuiqi, shugabar kungiyar 'yan kasuwan kasar Australia da ke kasar Sin ta gaya wa wakilinmu cewa, akwai kyakkyawar makoma a fannin hadin gwiwa a tsakanin kamfanonin kasashen Australia da Sin. Ta kara da cewa,

"A ganina, akwai zarafofi da yawa a cikin wannan babban shiri. Kamfanonin kasar Australia sun nuna fifiko a fannin samar da muhimman ababen more rayuwa, da ba da hidima a fannin hada-hadar kudi. Ban da wannan, yarjejeniyar yin cinikayya maras shinge a tsakanin kasashen biyu ta samar da dimbin zarafofi wajen hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin ayyukan gona, da sha'anin kudi. Amma ina son hadin gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin wajen raya ayyuka a ketare musamman ma a yankunan da shirin 'ziri daya da hanya daya' ya shafa."

Jakadun kasashe da dama da ke kasar Sin su ma sun bayyana aniyarsu ta sa hannu a cikin wannan shirin. John Paul Kavanagh, jakadan kasar Ireland da ke kasar Sin ya bayyana cewa, shirin "ziri daya da hanya daya" wani shiri ne na karbar kowa, hakan ya shaida cewa, shirin ba zai shafi wasu kasashe kalilan kawai ba. kasar Ireland na da karfi wajen nazarin sabbin fasahohi, kuma ta nuna fifiko a fannonin ba da hidimar hada-hadar kudi, fasahohin zamani na ayyukan gona, da sadarwa, don haka tana maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar.

Haka zakila, masu halartar taron sun yi tsokacin cewa, sun kara fahimtar wannan shiri na "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar a yayin taron, suna kuma jiran inganta hadin gwiwa tare da Sin don samun nasara tare.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China