Mr. Rudd ya bayyana haka ne a jiya yayin taron dandalin tattaunawar ilmin kasar Sin da aka yi a birnin New York na kasar Amurka.
Haka kuma, ban da shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, Mr. Rudd yana ganin cewa, gwamnatin kasar Sin na da isasshen lokaci wajen tabbatar da ci gaban tattalin arziki ta hanyar yin amfani da manufofin da abin ya shafa, kana makomar gyare-gyaren kamfanoni mallakar gwamnati da kuma masu zaman kansu na da kyau, musamman ma ga kamfanonin ciniki na yanar gizo, wadanda za su kara karfi ga ci gaban kasar Sin na dogon lokaci.
Bugu da kari, Mr. Rudd ya kuma musanta masu ra'ayin da ke cewa, kasar Sin za ta fadi saboda raguwar saurin ci gaban tattalin arzikin kasar, ya ce, ra'ayin ba shi da wata madogara ta fasaha, sannan ba gaskiya cikin sa, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu ne sabo da tsarin yin gyare-gyare da kasar ke aiwatarwa da kuma yanayin tattalin arziki na ketare, sannan ya yi imani kan ci gaban tattalin arziki na kasar ta Sin. (Maryam)