A nasa bangaren kuma, Mr. Obiang ya bayyana cewa, ya amince da sharhin da shugaba Xi ya yi kan dangantakar dake tsakanin kasashen Equatorial Guinea da Sin. Ya kara da cewa, akwai dangantakar sada zumunta irin ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, kuma su kan goyi bayan juna da kokarta yin hadin gwiwa cikin adalci.
Sannan shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, a yayin taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka da aka shirya kwanan baya a kasar Indonesiya, an sake karanta ka'idoji 10 na daidaita huldar dake tsakanin kasa da kasa da aka tabbatar a yayin taron Bandung yau shekaru 60 da suka gabata. Kasar Sin ta dade tana goyon bayan kasashen Afirka a kokarin da suke yi na tabbatar da 'yanci da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwa. A kullum kasar Sin da kasashen Afirka suna kokari tare wajen kawar da wahalhalu da kuma neman samun ci gaba. Bunkasa dangantakar hadin gwiwa irin ta sada zumunta tsakaninta da kasashen Afirka ita ce babbar manufar diflomasiyya da kasar Sin take bi a kullum. Kasar Sin, wato kasa mai tasowa mafi girma da nahiyar Afirka, wato nahiya mafi girma dake kunshe da kasashe masu tasowa, dukkansu suna da damar samun bunkasuwa ga juna. Sakamakon haka, kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka na dacewa da babbar moriyarsu. Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 15 da kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Sabo da haka, bangaren Sin da bangaren Afirka za su yi aiki tare domin tsara shirye-shiryen yin hadin gwiwa na tsawon shekaru 3 masu zuwa, inda za a fitar da wasu sabbin matakan da za su biya bukatun bangarorin biyu.
Daga karshe, Mr. Obiang ya bayyana cewa, kasashen Afirka suna fuskantar kalubaloli masu tsanani wajen tabbatar da kwanciyar hankali da neman ci gaba. Ya kuma gode da bangaren Sin da ya kan taimakawa kasashen Afirka ba tare da gindaya wasu sharuda ba, wannan yana da muhimmanci sosai ga bunkasuwar kasashen Afirka bisa sabon yanayin da ake ciki yanzu. (Sanusi Chen)