Rahotanni daga Togo, na nuna cewa, shugaban kasar mai ci Faure Gnassingbe ne ke kan gaba, a sakamakon zaben kasar da aka kada ranar 25 a watan nan.
Alkaluman farko da hukumar zaben kasar ta fitar sun nuna cewa, Gnassingbe, ya shige gaban sauran 'yan takara 4 dake neman kujerar shugabancin kasar, da kuri'u 133,375, yayin da mai biye da shi Jean-Pierre Fabre ke da kuri'u 68,957.
Alkaluman sun kuma nuna cewa, Mouhamed Traore, ya samu kuri'u 1,761, yayin da Gerry Taama ke da 1,657, sai kuma Aime Gogue da ya samu kuri'u 1,569.
Wannan sakamakon dai ya shafi runfunan zabe 934 dake mazabun kasar 6 ne kadai, cikin jimillar mazabu 42.
Kimanin 'yan kasar ta Togo miliyan 3 da rabi ne dai suka kada kuri'unsu a zaben na wannan karo, wanda kuma zai baiwa wadanda ya lashe shi damar kasancewa shugaban kasar, tun daga bana ya zuwa shekarar 2020.
Tuni dai jami'an sa ido ga gudanar zaben suka bayyana kammalarsa cikin kyakkyawan yanayi, ba kuma tare da fuskantar wata babbar matsala ba. (Saminu)