Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Lahadin nan ya yaba a kan yadda aka tafiyar da babban zaben a kasar Togo cikin lumana.
A ranar Asabar ne dai al'ummar kasar miliyan 3.5 wadanda suka cancanci kada kuri'an suka kada kuri'unsu a tashoshin zabe 8,994 a daukacin fadin kasar mai al'umma miliyan 6.2 wadda take yammacin Afrika.
Kakakin magatakaradar a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, Mr Ban Ki-moon yana kira ga 'yan siyasa da sauran sassan daban daban na jama'ar kasar da su yi amfani da lokacin jiran sakamakon zaben su ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali da lumana yadda ya kasance a lokacin zaben.
Haka kuma Mr Ban ya bukaci dukkan 'yan takara da magoya bayansu da su warware rashin fahimta dake tsakanin su ta hanyar zuwa ga hukumomin shari'a.(Fatimah)