A jiya Lahadi, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta bayar da kayayyakin jinya da ake iya amfani da su cikin ceton gaggawa 4 da kuma kudin taimako a mataki na farko wanda yawansu ya kai dalar Amurka dubu 170 ga yankin dake fama da girgizar kasa a kasar Nepal, domin biyan bukatun mazauna wurin.
An ba da labari cewa, wadannan kayayyakin da hukumar ta bayar sun hada da magunguna da na'urori. Kowane kayan jinya din zai iya samar da hidimomin jinya ga mutane dubu 10 har nan da watanni 3. Hukumar WHO ta samar da wadannan kayayyakin jinya ne musamman ma domin amfani da su a yayin da aka rasa tsarin ba da jinya bayan bala'u.
A halin yanzu, hukumar tana taimakawa ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Nepal wajen ba da jinya ga wadanda suka ji rauni da kuma farfado da asibitoci da hukumomin kiwon lafiya da girgizar kasa ta lalata su.
Ban da haka kuma, hukumar ta bayyana cewa, ban da mutanen da suka ji rauni, mutanen da suka rasa gidajensu a yayin girgizar kasa su ma suna bukatar hidimar kiwon lafiya, kamarsu samun tsabtaccen ruwan sha da kashe kwayoyin cuta da dai sauransu.(Lami)