in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Yawan mutanen da suka mutu yayin girgizar kasa a Nepal ya kai 3218
2015-04-27 10:09:58 cri

A jiya Lahadi kasar Nepal ta shiga rana ta biyu bayan aukuwar girgizar kasa mai karfin digiri 8.1. A tsakiyar wannan rana, an sake samun girgizar kasa mai karfin digiri 7.1, wadda ta haddasa zubewar dusar kankara a dutsen Everest.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Nepal ta ba da labari cewa, ya zuwa daren jiya lahadin, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasa ta Nepal ya kai fiye da 3218, a yayin da mutane 6535 suka ji rauni. Kazalika, an tabbatar da cewa, akwai mutane 18 na kasashen waje da suka mutu a yayin da suka haura dutsen. A wannan rana kuma, rukunonin ceto da suka fito daga kasar Sin da kasashen Turai sun isa birnin Kathamandu domin ba da taimako.

Gwamnatin Sin ta tsai da kuduri cewa, za ta samar wa gwamnatin Nepal kayayyakin tallafi da darajarsu ta kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 20, ciki har da tantuna da barguna da na'urorin samar da wutar lantarki da kuma sauransu, domin nuna goyon baya ga aikin ceto sanadiyar girgizar kasar.

Rukunin ceto na kasar Sin ya isa birnin Kathamandu a jiya Lahadi ne, daga bisani, ya kafa tsarin tuntuba da daidaitawa tare da gwamnatin kasar. A safiyar yau Litinin, rukunin jinya na kasar Sin da ya hada da likitoci 58 ya tashi daga birnin Chengdu zuwa yankin dake fama da girgizar kasar a Nepal domin ba da taimakon jinya.

A sakamakon girgizar kasa, an kara samun mutuwar mutane a arewacin kasar Indiya dake iyakar kasa tsakaninta da Nepal da kuma arewa maso gabashin kasar.

Bisa kididdigar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Indiya ta gabatar, an ce, kawo yanzu mutane fiye da 60 a kasar sun mutu a sakamakon girgizar kasa.(Lami)

     

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China