A jiya Lahadi, aka yi zaben majalisar wakilan kasar Benin, inda 'yan takara fiye da 1600 da suka fito daga jami'yyu ko kawancen jam'iyyu 20 suka nemi mamaye gurabu 83 na majalisar. An dai fara jefa kuri'un ne daga safiyar ranar da karfe 7 zuwa yammacin da karfe 7 na yamma, sannan kuma aka fara aikin kididdiga.
An ba da labari cewa, kasar Benin na da mutane miliyan 4.47 da suka cancanci jefa kuri'u, an kuma kafa tasoshin jefa kuri'u 13,606 a yayin wannan zaben. Wa'adin sabbin 'yan majalisar wakilai zai kai shekaru 4. Wannan ne karo na 7 da aka yi zaben kafa doka bayan shekarar 1990 da aka gyara tsarin kasar. 'Yan majalisar wakilai dake kan gado za su kawo karshen wa'adinsu a ranar 15 ga watan Mayu na wannan shekara.(Lami)