Shuwagabannin kasashen Algeria da Benin, sun amince su hada gwiwa wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashensu a fannoni da dama, ciki hadda batun tsaro, da yaki da ayyukan ta'addanci.
Shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi ne ya bayyana wa manema labarai hakan, yayin ziyarar aikin kwanaki uku da ya gudanar, tare da tawagar manyan jami'an gwamnatinsa a kasar Aljeria.
Yayin ziyarar tasa, shugaba Yayi ya gana da shugaba Abdelaziz Bouteflika, da wasu manyan jami'an Aljeria, ciki hadda firaministan kasar Abdelmalek Sellal, da kuma kakakin majalissar dattawan kasar Abdelkader Bensalah.
Da yake karin haske game da sakamakon tattaunawar tasu, Yayi ya ce, baya ga batun tsaro, kasashen biyu sun amince su karfafa hadin kai a fannonin bunkasa sufurin sama da na ruwa, da inganta samar da wutar lantarki da iskar gas a Benin. Kaza lika sun amince da wani shiri na gudanar da hadin gwiwa tsakanin jami'o'in kasashen nasu.
A daya bangaren kuma, ministan tsaron kasar Benin Theophile Yaro, ya gudanar da shawarwari da mataimakin ministan tsaron Algeria Gaid Salah, game da hanyoyin fadada hadin gwiwar tsaro, musamman a wannan lokaci da barazanar ayyukan ta'addanci ke kara kazanta a yankunan Sahel, da na kudu da hamadar Sahara. (Saminu)