Kotun tsarin mulkin kasar Benin, babbar hukumar shari'a ta kasa a fannin dokokin tsarin mulki, ta tsai da niyyar shirya zaben 'yan majalisa a ranar 26 ga watan Afrilu mai zuwa, kana kuma zaben kananan hukumomi a ranar 31 ga watan Mayu mai zuwa. A cewar wannan matakin kotun, ya kamata a kafa sabuwar majalisar dokoki ta nan gaba a ranar 16 ga watan Mayun shekarar 2015. Daga nan ke nan, ya kamata a kira hukumar zabe a ranar 14 ga watan Febrairun shekarar 2015 domin ta shirya zaben 'yan majalisa a ranar 26 ga watan Afrilun shekarar 2015, in ji kotun.
Domin tabbatar da adalci da sahihancin wadannan zabuka, ana son wa'adin a kalla kwanaki 30 tsakanin zaben 'yan majalisa da zaben kananan hukumomi. Dalilin haka ne kotun ta dauki hurumin tsai da shirya zaben kananan hukumomi a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2015, in ji kotun. (Maman Ada)