in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da makon fina finan Sin a Benin
2015-02-12 14:10:58 cri

Darektan cibiyar yada al'adu ta kasar Sin dake Cotonou, hedkwatar tattalin arzikin kasar Benin, mista Bai Guangming, ya kaddamar a ranar Laraba da yamma a birnin Cotonou da makon fina finai na kasar Sin kan wasu kafofin talabijin na kasar Benin guda biyu ORTB da Ado TV.

Mun kaddamar da wannan makon fina finan kasar Sin kan wadannan kafofin talabijin din kasar Benin domin baiwa dukkan 'yan kasar Benin, maza da mata a duk inda suke, damar kusantar kasar Sin ta hanyar watsa fina finan kasar Sin kan ORTB da Ado TV a tsawon mako guda, in ji mista Guangming.

A cewar maitaimakin darektan kula da fina finan kasar Benin M. Mathias, fina finan wata babbar hanya ce ta yada al'adu. Makon fina finan na kasar Sin a nan kasar Benin namu ne, kuma wata muhimmiyar dama ta gano da duba abin da muke ji kan manufar ci gaba. Idan kasar Sin ta samu damar samun ci gaba har zuwa wannan matsayi na tabbatar da muhimmancin da kasar ta baiwa al'adunta, to ana ganin wani dalili ne gare mu a nan kasar Benin, mu bunkasa kasarmu tare da mai da hankali da koyi da kasar Sin, in ji jami'in gwamnatin kasar Benin tare da yin kira ga al'ummar kasar da su amfani da al'adu wajen samun ci gaba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China