in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen Sin ya yi kira ga MDD da ta taka rawa a jagorancin yaki da ta'addanci
2014-09-25 09:53:32 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, kamata ya yi MDD da kwamitin tsaron majalissar su taka babbar rawa wajen jagorancin yaki da ta'addanci a duniya baki daya.

Mr. Wang wanda ya fadi hakan a wajen babban taron majalissar game da ta'addanci ya yi nuni da cewa, yadda ta'addanci ya sake kunno kai ya kamata kasashen duniya su bi tsarin da aka san cewa zai ba da mafita tare da bin ka'idojin dokokin duniya da kudurori da suke tafiyar da huldar kasa da kasa.

Da fari dai Mr, Wang ya ce, ya kamata a tabbatar da hadin kai mai karfi. Yana mai bayanin cewa, MDD da kwamitin tsaron majalissar za su taka rawa wajen jagorancin yaki da ta'addanci, domin wannan ne kadai hanyar da za'a bi ta tabbatar da hadin kai, a kuma cimma burin huldar da juna yadda ya kamata.

Minista Wang ya ce, hanya ta biyu kuma da ya kamata a bi ita ce kasashen duniya su dauki hanyoyi daban daban masu karfi wajen tunkarar wannan lamari. Ya ce, yaki da ta'addanci a duniya baki daya kamata ya yi a bi shi ta cudanya a tsakanin kasashe da suka hada da ta fuskar siyasa, tsaro, tattalin arziki, sha'anin kudi, bayanan sirri da sauran dabaru, da nufin shawo kan alamu da kuma dalilan dake kawo ta'addanci, musamman idan aka tumbuke tushe da kuma wurin da ake kiwon wannan dabi'a. Ya kuma kara da cewa, ayyukan soji a wannan bangaren ya kamata su je daidai da ka'idojin MDD da sauran hukumomin tsaro.

Haka kuma Mr. Wang ya jaddada cewa, dole ne kasashen duniya su nace wajen bin hanyoyin yaki da ta'addanci.

Daga nan sai ministan ya jaddada muhimmancin aiki tare domin shawo kan barazanar ta'addanci da ake fuskanta, inda ya ce, kasar Sin ta rika ta bayyana matsayinta na kyamar duk wani nau'in aiki da ta'addanci, sannan za ta tsaya a kan hakan. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China