in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya cimma kuduri kan mayakan ta'addaci na kasashen waje
2014-09-25 14:56:47 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya amince a ranar Laraba da wani kudurin yaki da barazanar da 'yan ta'addan kasashen waje suke kawowa, ya kara fafada tilastawa kasashe mambobi dauka matakai domin fuskantar wannan bazarana.

Kudurin ya samu amincewar mambobi 15 na kwamitin tsaro bisa babban rinjaye a yayin wani zaman taron musamman da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya jagoranta, wanda kasarsa ke shugabantar kwamitin a watan Satumaban, kudurin na da manufar yin rigakafi da dakile ayyukan daukar mayaka, tsare-tsare, jigila da samar da kayayyaki ga wasu matune da suke da kamannin mayakan ta'adddanci na kasashen waje, musammam ma mutanen dake zuwa wata kasa da ba kasarsu ba, ko kasancewa masu daukar mayaka da shirya jigilarsu, ko shirya ayyukan ta'addanci.

Haka kuma kudurin yana kira ga dukkan kasashe mambobi na MDD da su daukar matakai domin yaki da wannan annobar, musamman ta yin rigakafin shiga tubar kaifin kishin islama dake ga ta'addanci da kuma daukar mayakan ta'addanci na kasashen waje.

Kudurin na jadadda cewa, ya kamata kasashe mambobi su hana duk wani da ake zargi da ta'addanci ya shiga kasashensu ko kuma yada zango.

Kana kwamitin ya bukaci kasashe mambobi da su ba da hadin kai tsakaninsu domin karfafa musanyar bayanai, kuma su taimaka waje gano mayakan ta'addanci na kasashen waje tare da kuma nuna goyon baya ga kasashe mambobi da su bullo da dabarun yaki da wata fatawa nuna kishin islama da za ta kai ga aikata ayyukan ta'addanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China