in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya bukaci daukar matakan dakile tushen ayyukan ta'addanci
2014-11-20 13:35:04 cri

Wata sanarwa da ofishin shugaban kwamitin tsaron MDD ya fitar, ta bayyana bukatar daukar matakan dakile yaduwar ayyukan ta'addanci tun daga tushe.

Sanarwar wadda aka fitar bayan zaman kwamitin tsaron na Laraba, ta tabbatar da cewa, abu ne mawuyaci, a iya kawo karshen ayyukan ta'addanci ta hanyar amfani da karfin tuwo, ko dabarun tsaro kadai. Don haka sanarwar ta bukaci daukar dukkanin matakai na bai daya, bisa tsarin hadin gwiwar kasashe, da yankuna da kuma shiyyoyi daban daban.

Yayin zaman kwamitin, an kuma tattauna kan al'amuran da suka jibanci matakai na hana 'yan ta'adda yin tafiye-tafiye, da musayar bayanai domin gano su.

Kaza lika kwamitin tsaron ya bayyana damuwa game da karuwar amfani da kafofin sadarwa kamar yanar gizo, wajen shigar da jama'a cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.

A nasa tsokaci yayin zaman na Laraba, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, kira ya yi ga kasashen mambobin kwamitin, da su zurfafa tunani game da dalilan da ke haifar da fadadar kungiyoyin 'yan ta'adda, da kuma hanyoyin magance ci gaban su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China