in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan kasar Sin da ke Tarayyar Najeriya ya gana da shugaban kasar mai jiran gado
2015-04-23 11:22:24 cri

Jakadan kasar Sin da ke Tarayyar Najeriya Gu Xiaojie, ya gana da Muhammadu Buhari, shugaban kasar mai jiran gado jiya Labara 22 ga wata, inda suka yi musayar ra'ayoyi game da huldar dake tsakanin kasashensu, da kuma batutuwan da suka fi jawo hankulan sassan biyu.

Jakada Gu ya isar da murnar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga Muhammadu Buhari bisa lashe zaben kasar da ya yi, ya kuma bayyana cewa, kasashen Sin da Najeriya na da zumuncin gargajiya mai zurfi, suna kuma hadin gwiwa sosai a fannonin raya muhimman ababen more rayuwa, da makamashi, da aikin gona, da sadarwa da kuma wutar lantarki.

Ya ce gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan raya huldarta da Najeriya. Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 10 da kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, Sin na fatan amfani da wannan zarafi, wajen ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba.

A nasa bangare, Muhammadu Buhari ya godewa shugaba Xi bisa taya shi murna, ya kuma jinjinawa babbar nasarar da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa. Ya kara da cewa, kasar Sin ta nuna babban goyon baya ga aikin raya Najeriya, kana kamfanoninta na ba da babbar gundummawa wajen bunkasa tattalin arziki, da al'ummar Najeriya.

Kaza lika shugaban mai jiran gado ya bayyana fatan Najeriya na ci gaba da karfafa, da raya huldar gargajiya tsakaninta da kasar Sin, da kuma inganta hadin gwiwarsu a dukkan fannoni don amfana wa jama'ar kasashen biyu. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China