in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar APC ta lashe zabukan gwamnoni a Nigeriya
2015-04-14 09:48:53 cri

Jam'iyyar zababben shugaban kasa ta APC a Nigeriya ta lashe zabukan gwamnoni da aka yi Asabar din da ya gabata a jihohi 29 daga cikin 36 na kasar baki daya, kamar yadda wata kididdgar a hukumance ta bayyana.

Kididdigar daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC a Litinin din nan ta nuna cewa, jam'iyyar ta APC ta lashe 19 a cikin 29 da aka gudanar, ita kuma jam'iyya mai ci yanzu ta PDP a baya ita ke da rinjaye a jihohin kasar.

Kamar yadda wani mamban jam'iyyar ta APC a jihar Osun, Olufisayo Kolawole ya yi bayani, hakan yana da kyau ga demokradiya a kasar. Ya ce, jam'iyyun siyasa ba za su saki jiki ba, za su yi kokari..

Ya zuwa ranar Litinin, ana ci gaba da harhada sakamakon na wasu jihohi, san nan kuma ba'a yi zabe a jihohin Edo, Ekiti, Ondo, Bayelsa, Kogi, Anambra da Osun ba, saboda wa'adin gwamnoninsu bai kare ba.

Zabukan na makon da ya wuce, an yi su ne cikin tsauraran matakan tsaro, sai dai bai samu yawan jama'a ba kamar yadda aka fito a zaben shugaban kasar, inda 'dan takarar jam'iyyar APC Muhammadu Buhari ya lashe zaben. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China