in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
INEC ta gyara na'urorin tantance masu zabe gabanin zaben karshen mako
2015-04-10 09:38:51 cri

Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta ce, ta gyara dukkanin na'urorin tantance masu kada kuri'u, wadanda suka ba da matsala yayin zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Maris.

A cewar sakatariyar hukumar ta INEC Augusta Ogakwu, za a yi amfani da wadannan dubban na'urori ne a zaben gwamnoni da 'yan majalissun jihohin kasar a gobe Asabar.

Ogakwu, ta kara da cewa, daukar wannan mataki na gyara dukkanin na'urorin zai magance matsalar jinkiri da aka samu a yayin zaben da ya gabata, wanda ya kai ga tsawaita zaben da kwana guda.

Tuni dai hukumar ta INEC ta aike da kayayyakin zaben da na'urorin tantance masu kada kuri'un zuwa jihohin kasar 31, gabanin bude runfunan zabe a gobe.

Ba za a gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Ekiti, da Edo, da Ondo, da Osun da Anambra ba, kasancewar an gudanar da zabe a wadannan jihohi ne tsakanin shekarun 2013 zuwa 2014, wanda hakan ke nuna gwamnoninsu ba su kai ga kammala wa'adin aikinsu ba tukuna. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China