in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
APC ta Najeriya ta samu wasu jihohi a zaben gwamnoni
2015-04-13 10:12:02 cri

Sakamakon zaben gwamnonin da aka kammala a tarayyar Najeriya a karshen makon nan na nuna cewa, jam'iyyar adawa ta APC ta samu wasu jihohi a zaben, inda a jihar Bauchi, 'dan takararta Mohammed Abubakar ya yi nasara da lashe kuri'u 654,934, abin da ya sa shi ya doke abokan hamayyarsa guda 9, har da na jam'iyya mai barin gwamnati PDP Mohammed Jatau da ya samu kuri'u 282,650, in ji jami'in zaben jihar Mohammed Faruk.

A tsakiyar arewacin kasar kuma jihar Kaduna, malam Nasir El-Rufai na jam'iyyar APC ya zama zakara a zaben gwamnan da kuri'u 1,117,635, inda ya doke sauran 'yan takara 14, ciki har da gwamna Ramalan Yero mai barin gado wanda ya samu kuri'u 485,833, kamar yadda jami'in zabe Jafar Kaura ya yi bayani.

Haka kuma tsohon shugaban majalissar wakilan Nigeria Aminu Masari shi ya lashe zaben a jihar katsina karkashin jami'iyyar APC da kuri'u 943,085, ya doke abokin hamayyarsa na PDP Musa Nashuni wanda ya samu kuri'u 476,768 a bayanin jami'in zaben jihar Lawal Bilbis.

A jihar Ikko kuwa, cibiyar hada hadar kasar 'dan takarar APC wanda daman jam'iyyar ke rike da jihar, Akinwunmi Ambode shi ya yi nasara da kuri'u 811,994 a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP Jimi Agbaje da ya samu kuri'u 659,788. Daga cikin kananan hukumomi 20, Akinwunmi na da 15, Agbaje na da 5.

Sai dai kuma a jihar Gombe dake arewa maso gabashin kasar, gwamna mai ci yanzu Ibrahim Dankwambo na jam'iyyar PDP ya sake samun nasarar zarcewa da kuri'u 285,369, inda ya doke abokin takararsa Inuwa Yahaya na APC mai kuri'u 205,132. Gaba daya daga cikin kananan hukumomi 11, Dankwambo ya samu 10, Yahaya na da 1, in ji jami'in zaben jihar Saminu Ibrahim.

Haka kuma a jihar Akwa Ibom, jam'iyyar PDP ce ta lashe zaben gwamnan nan, inda 'dan takararta Udom Emmanuel ya samu kuri'u 996,071 a kan abokin karawarsa na APC Umana Umana mai kuri'u 89,865, kamar yadda jami'in zabe James Epoke ya sanar, ya ce, Emmanuel ya lashe dukkanin kananan hukumomin jihar 31. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China