Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya, ta yi alkawarin baiwa sabuwar gwamnatin da aka zaba cikakken goyon baya, da gudummawa domin tallafawa ci gaban kasar baki daya.
Hakan dai na kunshe ne cikin kalaman kakakin gwamnatin mai barin gado Olisa Metuh, yayin wani taron manema labaru da ya gudana a Abuja, fadar gwamnatin kasar.
Metuh ya ce, jam'iyyar PDP za ta marawa sabon shugaban kasar Muhammadu Buhari baya, ba kuma za ta yi yinkurin yiwa sabuwar gwamnatin kafar ungulu ba.
Ya ce, PDP na fatan hadin gwiwa da sabuwar gwamnatin wajen daidaita al'amura a kasar, tare da ba ta cikakkiyar damar bunkasa kasa cikin nutsuwa.
Metuh ya kara da cewa, jam'iyyar tasu ta dauki wannan mataki ne duba da cewa, ci gaban kasar shi ne sama da duk wata jam'iyya ko burin wani mutum guda. (Saminu)