in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi jawabi a yayin taron koli na kasashen Asiya da Afirka
2015-04-22 16:46:20 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai kunshe da shawarwari uku yayin bikin bude taron koli na kasashen Asiya da Afirka dake gudana a birnin Jakarta, babban birnin kasar Indonesiya, taron da ya samu halartar shugabanni, da wakilan gwamnatoci na kasashe 77 daga Asiya da Afirka, tare da kuma wasu masu sa ido na sauran yankuna.

A shekaru 60 da suka wuce, an tsara wannan waka mai taken "Sannu Bandung", wakar dai ta musamman an shirya ta ne domin taron kasashen Asiya da Afirka. A yau bayan shekaru 60, yaran wurin sun sake rera wannan waka mai salon musamman na kasar Indonesiya, domin maraba da shugabanni masu halartar taron.

Shekarar 2015 shekara ce ta cikon shekaru 60 da kiran taron Asiya da Afirka na farko, wannan ne kuma karon na uku da shugabannin kasashen suka sake taruwa bayan taron koli na shekarar 2005, hakan dai ya jawo hankulan bangarori daban daban.

A yayin bikin bude taron, shugaban kasar Indonesiya, Joko Vidodo ya bayyana cewa, taron koli na kasashen Asiya da Afirka da aka kira a birnin Bandung a shekaru 60 da suka wuce, ya sanya kasashen Asiya da Afirka fahimtar ra'ayi na tsayawa duniya a matsayinsu na kasashe masu 'yancin kai, ya kuma kara wa jama'ar kasashen gwiwa wajen kokarta neman daidaito. A yau, shugabannin kasashen Asiya da Afirka za su sake ba da shawarwari, da tsara manufofi da nufin neman ci gaban yankunan Asiya da Afirka.

"A cikin kwanaki biyun nan, za mu lalubo bakin zaren warware matsalolin rashin daidaito a duniyar da muke ciki. Muna sa ran za mu iya warware matsalolin da ake fuskanta. Kasashen duniya na kallon ci gaban da muke samu, don ganin yadda muke shugabantar kasashen Asiya da Afrika wajen samu ci gaba tare da ragowar kasashen duniya."

A shekarar 1955, wakilai 304 da suka fito daga kasashen Asiya da Afrika 29, sun taru a birnin Bandung na kasar Indonesiya, don sanar wa duniya cewa, kasashe masu tasowa ya kasance wani babban jigo a dandalin duniya.

A cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a wannan rana, ya bayyana cewa, a karkashin inuwar ka'idoji 5 na zaman tare cikin jituwa da aka cimma a gun taron Bandung, an gabatar da ka'idoji 10 wajen daidaita dangantakar kasa da kasa, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga ci gaban hulda a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata. A sabon yanayin da ake ciki, akidar Bandung na da ma'anar musamman.

"Ya kamata mu habaka akidar Bandung, da kuma zurfafa shi, domin kafa wata sabuwar huldar kasa da kasa mai kawo moriya ga juna, da kara tabbatar da adalci kan tsarin kasashen duniya, da kuma raya al'ummar bil Adama gaba daya, ta yadda za a amfana wa jama'ar kasashen Asiya da Afrika, da kuma sauran kasashen duniya."

Xi Jinping ya yi kira ga kasashen Asiya da Afirka da su inganta hadin gwiwarsu, kana da kara sada zumunta a tsakaninsu. Ya kuma sa kaimi gare su wajen zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, da tsakanin kasashe masu tasowa, gami da tsakaninsu da kasashe masu wadata.

"Ya kamata ko wane bangare ya tsaya kan manufar amfanar juna, da samun ci gaba tare, don yin amfani da yanayin tattalin arziki a nahiyoyin Asiya da na Afirka, wadanda ke biya wa juna bukata, a matsayin wata damar taimakawa juna. Haka zalika, ya kamata kasashen Asiya da na Afirka su zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, da hadin kai tare da sauran kasashe masu tasowa dake nahiyoyin latin Amurka, da kudancin yankin tekun Pasific, da dai sauran waurare, musamman ma a fannin harkokin siyasa. Bugu da kari, kamata ya yi a sa kaimi ga kasashe masu sukuni don su cika alkawuran da suka yi na tallafawa kasashe masu tasowa, ba kuma tare da gindaya wani sharadi ba, ta yadda za a kafa wata sabuwar huldar abokai tsakanin kasashe daban daban cikin daidaito."

Shugaba Xi Jinping ya sake nanata cewa, bisa sabon yanayin da ake ciki, kasar Sin za ta nace ga kokarin habaka hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da na Afirka. Haka zalika, shugaban ya yi alkawarin cewa kasar ta Sin a bana, za ta daina karbar harajin kwastam kan kashi 97 % na kayayyakin da wasu kasashe mafiya fama da talauci da suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin suke shigarwa cikin yankunanta. Sa'an nan za ta ci gaba da samar da tallafi ga sauran kasashe masu tasowa, wanda zai kunshi samar da guraben samun horaswa ga mutane dubu 100, da kafa cibiyar hadin kan Asiya da Afirka ta kasar Sin, da dai makamantansu.

Baya ga hakan kuma, ana sa ran ganin an zartas da wasu takardu 3, da za su shafi nuna goyon baya ga Falasdinu, da karfafa huldar abuta tsakanin kasashen Asiya da na Afirka, da yada akidar Bandung, a wajen taron shugabannin kasashen Asiya da na Afirka dake gudana.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China