in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayin Bandung zai jagoranci makomar kasashen Asiya da na Afirka a nan gaba
2015-04-22 16:27:01 cri
A Larabar nan ne aka bude taron koli na kasashen Asiya da Afirka, wanda za a shafe kwanaki 2 ana gudanarwa a birnin Jakatar na kasar Indonesiya, inda za a kaddamar da takardar dake sake nanata ra'ayin Bandung. Hakan dai na nuna cewa ra'ayin Bandung na ci gaba da dacewa da sabon yanayin da duniyar ke ciki a fannonin siyasa da tattalin arziki, zai kuma jagoranci kasashen Asiya da na Afirka zuwa wata makoma mai kyau cikin hadin gwiwa.

An kira taron Bangung a yayin da ake samun babban sauyi a yanayin duniya. A baya lokacin yakin cacar baki, kasashen Asiya da Afirka da suka samun 'yancin kai, bayan kawar da mulkin mallaka ba da dadewa ba, sun fuskanci matsalar zabar hanyar da za su bi. A sa'i daya kuma akwai bambanci da sabani a tsakaninsu, sakamakon wasu matsalolin da suka shafi tsarin zamantakewar al'umma, da al'adu, da addinai, yankin kasashe, da tarihi da dai sauransu.

Daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Afrilu na shekarar 1955, shugabanni na kasashe 29 sun shirya taron kasashen Asiya da Afirka a birnin Bandung na kasar Indonesiya, inda suka tattauna kan ka'idojin huldar kasa da kasa. A yayin wannan taro karkashin kokarin da kasar Sin ke yi, an gabatar da ka'idar dake kunshe da a fannoni guda 10, wadda ta nuna ra'ayin Bandung na hadin kai da zumunci. Game da wannan batu, mataimakin shugaban sashen nazarin harkokin Asiya da tekun Pasific na kwalejin ilmin zaman takewar al'ummar kasar Sin mista Han Feng ya bayyana cewa,

"Ra'ayin Bandung na da ma'ana kwarai. Bayan yakin duniya na biyu, wata sabuwar adawa tsakanin manyan kasashe ta bulla, haka zalika ra'ayin mulkin mallaka da na tsarin siyasa da kasa daya ke da iko kan kasashe da dama na ci gaba da yin tasiri da duniya. A wannan yanayin da ake ciki, kasashe masu tasowa su na adawa da ra'ayoyin biyu, da kuma kokartawa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a duniya, da nufin neman bunkasuwarsu da 'yancin kai.

Kana kasashen sun tsara babbar manufar da ta shafi burin samar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa, wato manufar Bandung dake kunshe da fannoni guda goma. Haka nan an amince da rawar da kasashe masu tasowa ke takawa a dandalin duniya, da sabon yanayin da suke ciki, da kuma ra'ayin da suke bi."

Wannan manufar ta aza harsashi mai kyau wajen kafa sabon tsarin siyasa da tattalin arzikin duniya mai adalci yadda ya kamata, ita ma ta kasance babbar ka'ida ta huldar kasa da kasa.

A yau bayan shekaru 60, ana cikin wani muhimmin lokaci na juyi a tsarin duniya. Yanzu kasashen Asiya da na Afirka suna matsayi na gaba a fannonin samun makomar bunkasuwa a nan gaba, inda wadannan kasashe suka riga suka kai sama da rabi a cikin kasashe mambobin MDD. Amma, duk da haka ra'ayin neman mallakar duniya, da siyasar nuna karfi, da kuma ra'ayin ta'addanci, na gaba wajen kawo tasiri ga zaman lafiya da zaman karko a duniya. Bayan haka kuma kasashen Asiya da na Afirka na da babbar dawainiya ta bunkasa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a.

Game da tasowar kasashen, a yayin da kasashe masu ci gaba ke kokarin kawo illa ga ci gaban sabbin manyan kasashe da tattalin arzikinsu ke bunkasa, a sa'i daya kuma suna da nufin kafa wani sabon tsarin siyasa, da tattalin arziki na duniya, domin tabbatar da matsayinsu na nuna fifiko. Mataimakin shugaban kwalejin harkokin diplomasiyya na kasar Sin, shehu malami Wang Fan ya nuna cewa,waccan manufa ta Bandung dake kunshe da fannoni guda goma, na dacewa da huldar kasashe duniya a sabon yanayin da ake ciki. Ya ce,

"Ko da yake yanayin duniya ya samu babban sauyi, a daya bangaren manufar ci gaba da dacewa na nan yadda take. Wadannan ka'idojin dake cikin manufar sun dace ga neman ra'ayi bai daya, tare da la'akari da bambanci, da zaman lafiyar juna, da kuma nuna girmawa ga juna. Bisa wadannan ka'idoji ne za a samu tabbaci, a fannin magance matsalolin dake da alaka da dangantakar kasashen duniya, da ma fannin warware muhimman matsaloli, a fannin neman bunkasuwa tare." (Bilkisu).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China