Bayan da aka kafa tsarin inshorar ajiye kudi a banki, za a kara bada tabbaci ga tsarin hada-hadar kudi na kasar Sin, da kara karfin yin takara da bada hidima na bankunan kasar. An gudanar da tsarin inshorar ajiye kudi don tabbatar da moriyar masu ajiye kudi, da kyautata tsarin tsaron hada-hadar kudi na kasar Sin, da kuma kafa tsarin tabbatar da yanayin hada-hadar kudi na kasar a cikin dogon lokaci. Hakazalika kuma, za a kara bada tabbaci ga tsarin bankunan kasar, da sa kaimi ga bankuna da su yi kwaskwarima, da inganta karfinsu na samun bunkasuwa da yin takara da kuma bada hidima. (Zainab)