in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin ya gana da shugaban majalisar wakilan kasar Habasha
2015-04-07 21:04:03 cri

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Yu Zhengsheng ya gana da shugaban majalisar wakilan kasar Habasha Kassa Teklebirhan a yau Talata 7 ga wata a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar, Mr. Yu ya ce, wannan shekara ta cika shekaru 45 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, don haka Sin na fatan kara hadin gwiwa da Habasha don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma bude sabon shafi na dangantakar kasashen biyu.

Yace Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin na mai da muhimmanci sosai kan batun yin mu'ammala da hadin gwiwa tsakaninta da majalisar wakilan Habasha.

A nasa bangare, Mr Kassa Teklebirhan ya nuna matukar godiya ga taimakon da Sin take baiwa kasar a fannoni daban-daban na lokaci mai tsawo, yana kuma fatan kara samun fahimtar juna tsakaninsu da zurfafa zumuncinsu da kuma sa kaimi ga hadin gwiwa tsakaninsu a dukkan fannoni. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China