in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yu Zhengsheng ya kai ziyara kasar Algeria
2014-11-03 15:53:10 cri
Bisa gayyatar da shugaban majalisar al'ummar kasar Algeria Abdelkader Bensalah ya yi masa, shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng, ya isa kasar Algeria domin gudanar da ziyarar aiki daga ranar 1 zuwa 3 ga watan nan na Nuwamba.

Tuni dai Mr. Yu ya gana da shugaba Abdelaziz Bouteflika, da firaministan kasar Abdelmalek Sellal, da shugaban majalisar dokokin jama'ar kasar Mohamed Larbi Ould Khalifa, da kuma ministan harkokin wajen kasar Ramtane Lamamra. Kana Yu Zhengsheng ya tattauna da Abdelkader Bensalah.

Mr. Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci karai ga dangantakar hadin gwiwa, da sada zumunta tsakaninta da kasar Algeria, tana kuma fatan hadin gwiwa tare da kasar Algeria wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito kansu, tare da kara mu'amala a tsakaninsu a dukkan fannoni.

A nasu bangare shugaba Bouteflika, da shugaban majalisar al'ummar kasar Bensalah, da sauran shugabannin kasar sun jinjinawa kasar Sin, bisa goyon bayanta, da taimakon da take baiwa kasar cikin tsahon lokaci. Kaza lika Algeria na fatan ci gaba da raya dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasar Sin a dukkan fannoni, da kara yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa, da yankuna domin inganta dangantakar dake tsakaninsu cikin sauri a kuma dukkanin fannoni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China