in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen sama yaki na Kenya sun jefa bam a sansanoni biyu na al-shabab a kudancin somaliya
2015-04-06 20:22:18 cri
Rahotanni daga Nairobi babban birnin kasar Kenya na cewa jiragen yakin kasar sun kai hari da bam a sansanoni biyu na kungiyar al-shaabab tare da hallaka mutane da dama inji majiyar sojin kasar..

Kakakin rundunar tsaron kasar David Obonyon yace jiragen yakin sun kai harin ne da bam a sansanonin ne dake yankin Gedo a kudancin Somaliya da yammacin ranar Lahadin nan zuwa wayewar garin litinin .

David Obonyo yace mayakan kungiytar da dama sun halaka a lokacin harin inda bayanai da ke zuwa ya nuna cikin har da wassu manyan jami'an su a lokacin da jiragen yakin suka jefa bama baman a wajen.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China