in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daya daga cikin mahara na jami'ar Kenya yaron wani kusa ne a kasar
2015-04-06 17:27:05 cri
Mahukuntan kasar Kenya sun tantance daya daga cikin mahara 4 da suka afka ma jami'ar Garissa na kasar tare da hallaka mutane 148 ranar alhamis din data gabata.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida Mwenda Njoka ya bada sunan Abdirahim Abdullahi , dan wani basaraken Mandera a matsayin daya daga cikin mahara, wanda kuma ya kammala karatun shi na lauya a jami'ar Nairobi.

Abdullahi da tabbas 'yan uwa da abokai suka gane shi, an ce ya bar gida Kenya tun a shekarar 2013 kuma Mahaifin shi ya sanar ma 'yan sanda cewar 'dan na shi ya bace basu ganshi ba kuma ya bayyana damuwar mai yiwuwa ne ya tsallaka zuwa Somali don ya shiga kungiyar Al-shaabab.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China