in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar APC a Najeriya ta yi allawadai da harin ta'addanci a Kenya
2015-04-05 17:44:47 cri
Babbar jam' iyyar APC a Najeriya ta yi allawadai da harin ta'addancin da aka kai a jami'ar Moi da ke garin Garissa a kasar Kenya wanda ya halaka mutane 148 tare da jikkata wasu da dama.

Jam'iyyar ta bayyana kungiyar Al Shabab ta kasar Somaliya da ta dauki alhakin kai harin, a matsayin kungiyar masu kaifin kishin islama da ba a bukatarta a wannan duniya.

A cewar wannan sanarwa, ta'addanci ya zama babban kalubale ga duniya, dole ne kasashen duniya su maida hankali sosai wajen kawar da duk wani nau'in ta'addanci, kuma ko kadan 'yan ta'adda ba za su samu wurin da za su buya ba.

Jam'iyyar APC ta isar da ta'aziyarta ga gwamnati da al'ummar Kenya baki daya tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China