Ofishin firaministan kasar Singapore ya fitar da sanarwar rasuwar tsohon firaministan kasar Lee Kuan Yew. Sanarwar dai ta ce Mr. Lee ya rasu ne a jiya Lahadi a wani babban asibitin kasar da misalin karfe 3 da minti 18 na safe, yana da shekaru 91 a duniya.
Sanarwar ta ce, tuni babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya fidda sanarwar jaje game da rasuwar tsohon firaministan, yana mai nuna alhininsa ga iyalai da kuma gwamnati, da jama'ar kasar Singapore.
Kaza lika sanarwar ta bayyana Lee Kuan Yew a matsayin muhimmin mutum a nahiyar Asiya, inda cikin shekaru 30 da ya yi yake gudanar da harkokin siyasa, kasar Singapore ta daga matsayin kasa mai tasowa zuwa wadda ta ci gaba, wadda kuma ta kasance cibiyar kasuwanci ta kasa da kasa.
Sanarwar ta ce Ban Ki-Moon ya jinjinawa kyakkyawan hadin gwiwar dake tsakanin gwamnatin Singapore da MDD, tare da fatan alheri ga zurfafa huldar kawance a nan gaba.(Lami)