in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta sanar da daukar nauyin kai farmaki a kasar Tunisiya
2015-03-20 14:46:55 cri

Kafofin watsa labaru na kasar Tunisiya sun bayar da labarin cewa, kungiya mai tsattsauran ra'ayi ta IS ta watsa wata muryar da aka dauka kan shafin yanar gizo na internet, inda ta sanar da daukar nauyin kai farmaki a dakin ajiye kayayyakin tarihi na Bardo dake kusa da babban ginin majalisar dokokin kasar Tunisia a ranar 18 ga wata.

Ban da haka kuma, an ce, kungiyar IS ita ma ta nuna wani rubutaccen bayani ta shafin yanar gizo na internet, inda ta sake sanar da daukar alhakin kai wannan hari.

Haka zalika, a cewar fadar shugabancin kasar Tunisiya, sojojin kasar sun cafke mutane 9 da ake zarginsu da laifin kai wannan hari a ranar 19 ga wata, kuma ana ganin cewa, mutane 4 daga cikinsu na da alakar kai tsaye da wannan hari.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Tunisiya ta sanar da sakamakon kididdiga a ranar 19 ga wata cewa, farmakin da aka kai wa dakin ajiye kayayyakin tarihi na Bardo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23, da suka hada da 'yan kasar Tunisiya 3 da masu yawon shakatawa 20 da suka fito daga kasashe daban daban.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China