in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe runfunan zabe na zaben shugaban Tunisiya zagaye na 2
2014-12-22 14:40:48 cri

Runfunan zabe na yankuna 27 na dukkan fadin kasar Tunisiya sun rufe a ranar Lahidi da misalin karfe shida na yamma bisa agogon wurin domin ba da hanya kan ayyukan kidayar kuri'un zabe na zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Tunisiya. Bayan karfe hudu na yamma, adadin wadanda suka kada kuri'a ya zarce kashi 56 cikin 100 a cikin runfunan zabe dubu hudu, a yayin da wasu runfunan zabe 138 ba su ba da adadin yawan mutanen da suka kada kuri'a ba. A cewar alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta (ISIE) ta bayar a yayin wani taron manema labarai a cibiyar dake kula da harkokin zaben shugaban kasa dake birnin Tunis.

Bayan sun wuce zagayen farko na zaben shugaban kasa tare da kowanensu kashi 39,46 cikin 100 da kuma kashi 33,43 cikin 100, tsohon faraministan kasar Beji Caid Essebsi wanda kuma ya lashe zaben 'yan majalisu da shugaba mai barin gado Moncef Marzouki suka fafata zagaye na biyu.

Hukumar (ISIE) ta sanar a ranar cewa, za ta yi duk wani kokarinta domin fitar da sakamakon wucin gadi a cikin sa'o'i ishirin da hudu bayan kammala zaben, wato a ranar Litinin 22 ga watan Disamba. Don haka ISIE tana da kwanaki uku na amsa kararrakin 'yan takarar biyu, kafin ta fitar da sakamakon zabe na din din din. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China