in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban MDD ya nuna yabo da zaben shugaban kasa a Tunisiya
2014-12-24 10:52:04 cri

Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon, ya bayyana yabonsa a ranar Talata ga al'ummar kasar Tunisiya kan yadda suka gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a ranar 21 ga watan Disamba cikin nasara. A cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa, mista Ban ya kuma isar da sakon taya murna ga Beji Caid Essebsi kan nasasar da ya samu na kasancewa shugaban kasa bayan wannan zaben.

Babban abin tarihi ne da ya faru, kuma muhimmin mataki na dorewar kasar bisa tsarin demokaradiyya, hakan kuma ya tabbatar da bukatar al'ummar Tunisiya na zaben gwamnati mai kishin kasa da kuma wakiltar al'ummar Tunisiya baki daya, in ji shugaban MDD.

Mista Ban ya bayyana fatan ganin al'ummar Tunisiya da sabbin hukumomin da aka zaba su ci gaba da bin wannan tsarin na demokaradiyya. Daga karshe, mista Ban ya jaddada wa sabon shugaba Beje Caid Essebsi goyon bayan MDD. Mista Essebsi mai shekaru 88 da aifuwa ya kasance shugaban kasar Tunisiya na farko da 'yan kasar suka zaba cikin 'yanci bisa tsarin demokaradiyya tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta a shekarar 1956. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China