in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta taya Tunisiya murnar kammala babban zabe cikin lumana
2015-01-16 10:01:57 cri

Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Madam Nkosazana Dlamini Zuma ta mika sakon taya murna ga kasar Tunisiya game da kammala babban zabenta cikin nasara da kwanciyar hankali.

A cikin wata sanarwa da aka fitar daga cibiyar kungiyar, Madam Zuma ta kuma taya zababben shugaban kasar Beji Caid Essabsi murnar lashe wannan zabe da aka yi na farko tun juyin juya halin kasar a shekarar ta 2010.

Madam Nkosazana Zuma ta ce, kammala zaben cikin nasara, wata alama ce dake nuna himman 'yan kasar na ganin an kafa demokradiya, kuma wata alama ce dake nuna cewa, za'a iya sake ynnkuro da demokradiya bayan juyin juya hali.

Bayan jinjinar da ta yi wa shawarwarin da tawagar sa ido ta kungiyar ta bayar da ba da kwarin gwiwwa ga gwamnatin kasar Tunisiyan, shugaban kwamitin ta AU ta jadadada kudurin kungiyar wajen ba da cikakken goyon baya ga gwamnati da kuma al'ummar kasar ta Tunisiya.

Daga nan sai ta bukaci sabuwar gwamnatin da ta hanzarta kawo ci gaba ga tattalin arzikin kasar da kayayyakin walwalar al'umma baki daya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China