in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar tsaron Najeriya ta jinjinawa kwazon rundunar sojin kasar
2015-03-18 10:17:59 cri

Majalisar tsaron Najeriya ta jinjinawa kwazon rundunar sojin kasar, bisa da nasarorin da take samu, a yaki da take yi da dakarun kungiyar Boko Haram.

Yayin wata ganawa da manema labaru a jiya Talata, babban hafsan sojojin kasar Laftana Janar Kenneth Minimah, ya ce, taron majalisar tsaron wanda shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta, ya yi na'am da irin nasarorin da aka cimma a jihohin Borno, da Yobe da kuma Adamawa, jihohin da rikicin Boko Haram ya fi shafa.

Ya ce, yanzu haka sojojin Najeriyar sun kwato dukkanin yankunan da Boko Haram ke rike da su a jahohin Yobe, da Adamawa, da ma na jihar Borno, in ban da kananan hukumomi 3, wato Abadam, da Kalabaldi da kuma Gwoza.

Sai dai a daya hannun Minimah ya bayyana shakku game da yiwuwar gudanar da zabuka a yankunan da aka kwato. Ya ce, hukumar zaben kasar ce ke da alhakin zartas da hukunci game da hakan.

Makwanni kusan 5 ke nan, tun bayan dage manyan zabukan kasar da aka yi, inda a yanzu aka sanya ranar 28 ga watan nan na Maris ta zamo ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalissar tarayyar kasar. Yayin da kuma zaben gwamnoni da na 'yan majalissar jihohi zai biyo baya a ranar 11 ga watan Afirilu mai zuwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China